Al-Shabab ta kai hari Shalkwatar leken asiri

Hakkin mallakar hoto
Image caption Al-Shabab ta sha alwashin zafafa hare harenta a watan Ramadan

Rahotanni daga Somalia na cewa wani fada ya barke a babban birnin Kasar ma Mogadishu bayan fashewar wani abu kusa da Shalkwatar hukumar leken asiri

Jami'an Somalia sunce mayaka daga kungiyar al-Shabab sun farma wani gini kusa sa Shalkwatar leken asirin, inda suka musanta ikirarin da Al-Shabab din suka yi na cewar sun sami damar kutsa kai cikin ginin hukumar leken asirin kanta

Al Shabab ta lashi takobin zafafa yakinta da gwamnatin Somalia mai samun goyan bayan kasashen Yamma a lokacin azumin watan Ramadana wanda aka soma ranar Laraba