Ana ba-ta-kashi a majalisar Afghanistan

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda sun ce sun dakile yunkurin da 'yan bindiga suka yi na kutsa kai cikin majalisar dokokin.

A Afghanistan, ana can ana ba-ta-kashi a cikin majalisar dokokin kasar.

An tayar da bama-bamai a wajen ginin majalisar a lokacin da 'yan bindiga ke kokarin kutsa kai cikin majalisar.

'Yan sanda sun ce sun dakile masu kokarin shiga majalaisar dokokin, wadanda a yanzu haka suka ja-daga a wani ginin da ke daura da majalisar.

Shafukan sada zumunta na zamani sun nuna hotunan majalisar dokokin ya turnike da hayaki a lokacin da 'yan majalisar ke kokarin kwashe kayansu domin ficewa daga cikin ta.

Har yanzu dai ana ci gaba da jin karar fashe-fashen rokoki da gurneti-gurneti.

Kungiyar Taliban ta ce za ta kai hari a majliasar domin hana 'yan majalisar amince wa da nadin da aka yi wa sabon ministan tsaron kasar.

Rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce mutane da dama sun ji rauni.

Wannan lamari dai na faruwa ne a lokacin da ake watsa zaman majalisar kai-tsaye ta kafafen watsa labarai.