Zan yi wa Buhari biyayya — Atiku

Image caption Atiku Abubakar ya ce ya kamata a goyi bayan Buhari domin ya yi wa Najeriya aiki.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce zai yi wa Shugaba Muhammadu Buhari biyayya dari bisa dari.

Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ofishin watsa labaransa ya aikewa manema labarai ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, "Atiku Abubakar yana kallon Buhari da matukar kima, kuma zai yi masa biyayya sannan ya taimaka masa a kowanne lokaci a matsayin sa na shugaban kasa."

Sanarwar na zuwa ne a lokacin da ake rade radin cewa Atiku Abubakar na da hannu a zaben Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawan kasar, duk da yake jam'iyyar APC ba shi take so ba.

A cewar Atiku, bai kamata 'yan jam'iyyar APC su fara adawa da junansu ba tun ma ba a fara harkokin gwamnati gadan-gadan ba.

Ya bukaci 'yan jam'iyyar tasu su mara wa Shugaba Buhari baya domin ya fitar da Najeriya daga kangin da take ciki.