An kashe mutane hudu a Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza

'Yan sanda a Burundi sun ce an kashe mutane hudu sannan kusan mutane talatin suka jikkata a hare-haren gurneti da aka kai ranar Lahadi da dare.

Hare-haren sun afku ne a garuruwa uku, wadanda suka hada da Bujumbura, babban birinin kasar.

'Yan sanda sun ce magoya bayan 'yan adawan da ke so a hana zaben shugaban kasa da za a yi ne suka harba gurnetin.

A ranar Juma'a da dare 'yan sanda goma sha daya ne suka jikkata a hare-haren gurneti da aka kai a lokaci daya.