Ana bikin yanka karnuka a China

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana sa ran za a yanka kusan karnuka 10, 000 domin cin naman su.

A kasar China, an fara gudanar da bukukuwan shekara-shekara na yanka karnuka, a daidai lokacin da masu kare hakkin dabbobi ke kokawa kan lamarin.

Kafafen watsa labarai na kasar sun rawaito cewa za a yanka karnuka kimanin 10,000 domin a ci namansu a wajen bikin, wanda ake gudanarwa a lardin Guangxi a ranakun Lahadi da Litnin.

Wata tsohuwar malamar makaranta ta ja hankulan kafafen watsa labarai bayan ta sayi karnuka da dama domin ta hana a yanka su.

Mutanen da ke gudanar da bukukuwan sun ce ana yanka karnukan ne ta hanyar da ta dace.

Masu kare hakkin dabbobi sun ce ana wulakanta karnukan kafin a kashe su, kuma kusan mutane 3.8m ne suka sanya hannu a kan wata takarda domin yin Alla-wadai da wannan biki.