Turai za ta rage yawan 'yan ci-rani

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan ci rani

Ministotin waje na Tarayyar Turai sun amince su kaddamar da sabon shiri da zai rage yawan 'yan ci-rani da ke shiga kasashensu ta tekun Baharrum.

Za a yi amfani da jiragen sama da na ruwa, da kuma jiragen sama marasa matuki domin tattaro bayanan sirri domin a dakatar da mutanen da ke da hannu a safarar dubban mutane zuwa turai daga arewacin Afrika.

Alkaluma sun bayyana cewa 'yan gudun hijira 100, 000 ne suka yi irin wannan tafiyar a wannan shekarar.

An yi amanna mutane a kalla dubu biyu ne suka nutse a cikin teku.