Bashi: Girka ta gabatar da shawarori

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Firayiministan Girka Alexis Tsipras

Wani babban jami'in hukumar Tarayyar Turai ya ce shawarorin baya-bayan nan da Girka ta gabatar dangane da sarkakiyar basussukan da ake binta zasu taimaka wajen samar da mafita a wajen taron gaggawa da za a yi a Brussels.

Tarayyar Turan da asusun bada lamuni na duniya sun karbi sabbin shawarorin, sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken abinda shawarorin suka kunsa ba.

Shugabannin kasashen tarayyar Turan 19 zasu gudanar da taron gaggawan ne saboda matsin lamba da suke fuskanta na ganin Girkan bata saba biyan basussukan da ke kanta ba a yayin da wa'adin 30 ga wannan wata na Yuni ke kara kawo jiki.

Idan Girkan da kasa cimma yarjejeniyar baiyan asusun bada lamuni bashin da yakai dala biliyan 1 da miliyan 700 zuwa karshen watan Yuni, hakan zai iya fidda kasar daga cikin kungiyar kasashen masu amfani da kudin Euro.

Girka ta ce ta ce manufar sabbin shawarorin da ta gabatar, ita ce a samar da masalaha ga kiki kaka dake tsakaninta da wadanda suka bata basussuka.