Shirin samar da ruwan sha a Kenya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta

Gwamnatin Kenya ta kaddamar da wani shiri na samar da ruwan sha mai inganci ga al'umar kasar da ke zaune a unguwannin marasa galihu, wanda za su dinga saye ta hanyar amfani da katin kudi.

An dai kafa wasu cibiyoyin sayar da ruwan sha a unguwannin, kuma da zarar an sanya katin kudi a cikin na'urar sai ruwan sha mai tsabta ya zubo a kan farashi mai rahusa.

A baya mazauna unguwannin marasa galihun sun yi fama da matsalar rashin ruwan sha, inda suke saya daga 'yan ga-ruwa da tsadar gaske.