Ungozomomi na fuskanta matsala a Birtaniya

Shugabannin kungiyoyin kwadagon Biritaniya sun yi gargadin cewa sabuwar dokar shige-da-fice za ta tilasta wa dubban kananan ungozomomi 'yan kasashen waje da ke aiki a kasar komawa kasashensu na asali.

Hakkin mallakar hoto science photo library
Image caption Unguwar zomomi na fuskanta matsala a Biritaniya.

An fitar da wani tsarin da duk wani dan ci-rani dole ya bar Turai bayan shekaru shida idan albashinsa bai kai £35,000.

Jami'ar da ke koyar da Ungozomomi ta Royal College of Nursing (RCN), ta ce wannan sabuwar doka za ta janyo wa ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar hargitsi da kuma bata kudi wurin daukar ma'aikata.

Ofishin cikin gida na Turai ya ce dokar za ta rage bukatar 'yan ci-rani da aikin karfi.

Wannan yunkuri yana cikin shirin da gwamnati ke yi domin dakile matsalar shigowar 'yan ci-rani Biritaniya amma kungiyar kwadagon ta ce tana zaton kafin shekara 2017 matsalar za ta shafi a kalla ungozomomi 3,300.

Ungozomomi sama da 400,000 ne suke aiki da ma'aikatar kiwon lafiya ta Ingila.

Ana bukatar ungozomomi

Sakataren jami'ar RCN, Peter Carter, ya ce "Dokar 'yan ci-rani da aka fitar za ta janyo wa hukumar kula da lafiya ta NHS da ma wasu kungiyoyin samar da lafiya hargitsi. Ingila ta nemi a tsaurara matakan daukar ma'aikata 'yan ci-rani a daidai lokacin da ake da bukatarsu".

Ya kuma shaida wa BBC cewa wannan doka ba dabara ba ce, saboda a halin yanzu akwai karancin ungozomomin da ya haddasa daukar dubban ma'aikata daga kasashen waje.

Dr Carter ya kara da cewa yawancin ungozomomin ba su daukar albashin da ya kai £35,000, domin duka-duka albashinsu ba ya wuce tsakanin £21,000 da £28,000 a shekara.

A cewar Dr. Carter, samun magance wannan matsala din-din-din shine a kara horon unguwar zomomi a Turai, amma kafin nan 'yan cirani su zasu cike gurbin.

Kakakin ofishin cikin gida na Birtaniya ya ce "Kamar yadda Firayi Minista ya yi bayani, gwamanati tana so ta rage bukatar ma'aikata 'yan ci-rani".

Ya kara da cewa, "mun canza dokar zama a Biritaniya tun shekarar 2011, saboda a samu bambanci tsakanin zaman ma'aikaci da zama na din-din-din".

Hukumar tattalin arziki ta ce matsalar ba za ta dauki lokaci ba tunda akwai karin masana'antun horar da ungozomomi, kuma kwamitin bayar da shawara a kan 'yan ci-rani ta saka na'urar gano wadanda ke da karancin ilimi a sana'ar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumar NHS ta na daya daga cikin manyan ma'aikatar Ingila, wacce ke daukar mafi yawan ma'aikata 'yan ci-rani.

Daga kungiyar likitocin Birtaniya, Dr. Mark Porter, a wani taron likitocin ya yi bayanin cewa, "Mun ji lokacin zabe 'yan siyasa na cewa 'yan ci-rani sun cike mana asibitoci da hukumomin kula da lafiya, to tabbas haka ne kuma duk su ne likitoci da ungozomomi da kuma masu shara da goge-goge har ma da masana kimiyya. Idan kuma babu su hukumar kula da lafiyar kasar zata nakasa".