Mutane biyu sun harbu da Ebola a Saliyo

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ebola ta hallaka mutane da dama a Saliyo

Mahukunta a kasar Saliyo sun tabbatar da cewa wasu mutum biyu sun harbu da cutar Ebola a Freetown, babban birnin kasar.

Da an yi tsammanin an kammala shawo kan cutar a birnin, ganin cewa an shafe makonni ba tare da samun wanda ya kamu da cutar ba.

Kakakin cibiyar da yaki da cutar Ebola a kasar yace lamarin na da matukar daga hankali kasancewar an rufe baki dayan sansanonin da ake kebe masu harbuwa da cutar.

Wakiliyar BBC ta ce an shiga damuwa sosai saboda an rufe dukkan wuararen kebe masu harbuwa da cutar ganin cewa ba a samun sabbin mutanen da ke kamuwa.

Ana dai fargabar cewa watakila cutar ta sake bazuwa saboda ta bulla a unguwar marasa galihu mai cunkoson jama'a.

Ana dai ci gaba da kamuwa da cutar Ebola a arewacin kasar ta Saliyo.