Mutane miliyan 3 sun rasa muhallansu a Iraki

Image caption Yara da mata su ne abin ya fi shafa

Mutane fiye da miliyan uku ne a Iraki suka fice daga gidajensu tun lokacin da aka soma yaki da kungiyar IS a shekarar 2014.

Hukumar da ke kula da kaurar jama'a ta duniya, IOM ta ce galibin wadanda suka fice daga gidajensu a lardin Anbar da ke yammacin Bagadaza suke, saboda a nan kungiyar IS ta kwace daukacin yankin.

Kusan mutane dubu dari uku ne aka tilastawa barin gidajensu cikin watanni biyu a bana, tun bayan da kungiyar ta kwace iko da garin Ramadi.

Hukumar ta IOM ta ce mutane fiye da miliyan biyu na samun mafaka a gidajen jama'a, a yayinda wasu fiye da dubu dari shida suka zaune a sansanoni.