Zafi ya hallaka mutane 700 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matasa a birnin Lahore na Pakistan na maganin zafi

Jami'an tsaro a Pakistan sun kafa sansanonin agajin gagawa a Karachi don taimaka wa al'umar kasar da ke fama da yanayi mai tsananin zafi.

Suna taimaka musu da ruwan sha da na mai da ni'imar jiki, wato ruwan gishiri da suga ga mabukata.

Asibitoci sun cika da marasa lafiya, yayin da dakunan hutu da wajen ajiyar gawa suke cunkushe.

Mahukunta sun ce kusan mutum dari bakwai ne suka mutu, galibi wadanda suka manyanta.

Mutanen kasar na fushi da mahukunta sakamakon yawan katsewar wutar-lantarki da ke hana jama'a amfani da na'urar sanayaya daki da fankoki.

Matsalar ta kara muni sakamakon faruwatar a daidai wannan lokaci da ake azumin Ramadana.