Rwanda ta nuna takaici kan tsare Karake

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Rwanda, Paul Kagame

Kasar Rwanda ta bayyana tsarewar da aka yi wa shugaban hukumar leken asirinta, Karenzi Karake a London da cewar abin takaici ne matuka.

An dai kama jami'in ne bisa zargin da ake masa na aika laifukan yaki, sakamakon wani bincike da kasar Spaniya ke yi a kan wasu kashe-kashen ramuwar gayyar kisan-kare-dangin da aka yi a Rwanda a shekarar 1994.

Kuma ana sa ran za a gurfanar da shi gaban kuliya a wannan makon.

Biritaniya dai kawa ce ga Rwanda, amma ta ce a shara'ance wajibi ne ta tsare Mr Karake.

A shekara ta 2008 ne, kasar Spaniya ta fara gudanar aka bincike a kan wadannan kashe-kashe, sai dai masu aiko wa BBC labarai sun ce ana kokwanto game da hujjar zargin da ake yi wa Mr Karake.

Kusan mutum dubu dari takwas ne mayakan Hutawa suka yi wa kisan kare-dangi, kuma galibinsu Tutsawa ne.