APC ta musanta matsin lamba a kan Oyegun

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Cif John Odigie-Oyegun shugaban jam'iyyar APC na kasa

Jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria ta musanta cewa gwamnonin jam'iyyar sun bukaci shugaban jam'iyyar na kasa Cif John Oyegun ya sauka daga mukaminsa.

Wasu jaridun Nigeria sun ba da rahoton cewar gwamnonin sun bukaci Oyegun ya yi murabus saboda rawar da ya taka a zaben shugabannin majalissun dokokin kasar.

Sanata Lawan Shu'aibu tsohon dan majalisar dattijai kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce zuki tamalle ne maganar cewa gwamnonin na APC sun yi wa jam'iyyar bara'a tare da kiran shugabanta Cif John Oyegun ya sauka daga mukaminsa.

"Bansan wanda ya ce shugaban jam'iyyar ya sauka ba, saboda wadannan gwamnonin tara sun ziyarce shi inda suka nuna goyon bayansu ga matsayin jam'iyyar kan batun shugabancin majalisar dokoki," in ji Shu'aibu.

An dai shafe daren ranar Talata ana ganawa tsakanin gwamnonin da shugaban kasa da kuma shugabannin jam'iyyar a Abuja kan lamarin.