Me CBN ke yi game da darajar Naira ?

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Babban bankin na CBN ya ce wasu 'yan kasuwa su nemi dalar Amurka da kansa.

A wani mataki na kauce wa faduwar darajar naira idan aka kwatanta da dalar Amurka, babban bankin Nigeria, CBN ya ce zai daina sayarwa wasu 'yan kasuwar kasar dalar Amurka.

Babban bankin na CBN ya kebe wasu hajoji 40 wadanda daga yanzu zai daina yi wa masu shigo da su kasar musayar naira da dalar Amurka, sai dai su nemi dalar da kansu.

'Yan kasuwar da lamarin ya shafa sun hada da masu shigo da shinkafa da siminti da jiragen sama da rodi da kujeru da tufafi da dai sauransu.

Hakan dai wani mataki ne kokarin rage yawan dalar Amurka da ake fitar da ita domin kasuwanci a kasashen waje.

Ko a cikin watan Afrilu ma, bankin CBN ya rage yawan kudaden da 'yan Nigeria ke kashewa da kantunansu na banki a kasashen waje duk a matsayin ragikafi ga kudin kasar watau naira.

Tun bayan da farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya, darajar naira ta fadi idan aka kwatanta da dalar Amurka abin da ya zaburar da bankin wajen daukar matakan gannin tattalin arzikin kasar bai shiga cikin mummunan yanayi ba.

Sai dai abin jira a gani shi ne ko wadannan matakai za su iya hana faduwar darajar naira musamman ganin cewa Nigeria na dogaro sosai ga kayayyakin da ake shigo da su daga kasashen waje.