IS tana gab da kwace Kobane

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fada ya kaure a Kobane tsakanin IS da Kurdawa

Rahotanni daga Syria na cewa dakarun kungiyar IS masu da'awar kafa daular musulunci suna gab da mamaye garin Kobane na kasar Syria da ke kan iyakar kasar Turkiyya.

'Yan kungiyar ta IS dai sun fara kai harin ne da mota dauke da bom a tsakiyar garin na Kubane.

Rahotanni sun ce 'yan kungiyar ta IS suna fafatawa da mayakan kurdawa al'amarin da aka ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Mayakan kurdawa dai sun kwato garin na Kobane ne daga hannun 'yan kungiyar IS a farko-farkon wannan shekarar bayan da suka samu goyon bayan dakarun kasar Amurka.