Nigeria za ta hada gwiwa da Amurka kan kwato kudi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Buhari ya ce kudin da Jonathan ya bari a asusu ba su taka-kara-sun-karya-ba.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnatinsa ta samu tabbaci daga Amurka da wasu kasashe domin kwato kudaden da aka sace, aka ajiye a kasashen.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da Sarkin Musulmin kasar, Muhammad Sa'ad Abubakar da wasu shugabannin musulmai suka kai masa ziyara a Abuja.

Ya kara da cewa daga yanzu zuwa watanni uku gwamnatinsa za ta nemo kwararan shaidu da ke nuna cewa an sace kudin kasar, an kai su kasashen waje.

Hakan, a cewar sa, zai sa kasashen su mayar wa Najeriya kudaden da jami'an tsohuwar gwamnati suka sace.

A ranar Litinin ne Shugaba Buhari ya ce kudaden da gwamnatin Shugaba Goodluck ta bari a asusun Najeriya ba su taka-kara-sun-karya ba.