Cutar Kwalara ta barke a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar amai da guduwa na kashe yara kanana

Majalisar Dinkin Duniya na gargadin cewa barkewar cutar amai da gudawa a Sudan ta Kudu ka iya shafar dubban yara kanana

Asusun tallafawa kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce mutane 18 ne suka mutu a watan daya gabata.

Yace akwai bukatar dala miliyan hudu da rabi cikin gaggawa domin aikin tallafawa wadanda cutar ta shafa.

UNICEF ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar ruwan saman da zai sauka mai karfi a watanni masu zuwa, wanda zai sa cutar ta kara saurin yaduwa.

Wakiliyar BBC ke nan take cewa an fara samun rahotan wanda ya kamu da cutar ne daga babban birnin kasar na Juba, kusan wata guda daya wuce.

Kuma tun daga wancan lokaci ne ake kara samun mutanen da ake zargin sun kamu, a cikin birnin da kuma kauyukan dake kusa da shi