Boko Haram: Amurka ta bai wa Nijar tallafi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabannin kasashen tafkin Chadi sun yi taro kan Boko Haram a Abuja

Amurka ta baiwa Nijar tallafin dala miliyan bakwai da rabi domin daukar dawainiyar dubban 'yan gudun hijiran Najeriya da ke kasar.

Gwamnatin ta Amurka za ta mika wannan kudi ga hukumomin agaji na majalisar dinkin duniya da wasu kungiyoyin agaji masu zaman kansu domin sarrafa shi a Nijar.

Haka nan kuma gwamnatin ta Amurka ta tallafa ma kasashen yankin tafkin Chadi da dala miliyan 38 a matsayin gudunmuwarta dangane da gwagwarmayar da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Mataimakiyar ministan harkokin wajen Amurka mai kula da 'yan gudun hijira da bakin haure Misis Catherine Wiesner ce ta bayyana haka yayin kammala wata ziyarar aiki da ta kai a kasar ta Nijar.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane kusan miliyan uku da muhallansu.