Shin Buhari zai iya magance cin hanci?

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Hukumar EFCC ce mai yaki da rashawa da cin hanci a Najeriya.

Jama'a da dama a ciki da wajen Najeriya, sun yi amanna cewa sabon shugaban kasar, Muhammadu Buhari yana da kima da karfin halin da gwamnatinsa za ta iya tunkarar cin hanci da rashawa gadan-gadan.

Sai dai kuma ana ganin dole sai gwamnatin tasa ta yi wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar (wato EFCC) gagarumin garambawul, domin ayyukan hukumar su kai ga murkushe matsalar yadda ya kamata.

Masu sharhi kan al'amura dai sun ce sai an sakarwa hukumar ta EFCC mara wajen yin aikinta ba tare da shisshigi ko tsoma baki daga gwamnati ba.

Sannan sun ce ya kamata a gyara kundin tsarin mulkin kasar wanda ya takaita shugabancin hukumar ga jami'an tsaro kawai.