"Amurka ta yi wa Faransa leken asiri"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Hollande da Obama

Shafin Wikileaks mai kwarmata bayanan sirri ya wallafa wasu bayanai da suke nuna cewa hukumar leken asiri ta Amurka ta leko asirin shugaban Faransa Francois Hollande da magabatansa biyu, Sarkozy da Jacques Chirac.

An yi zargin leken asirin ya faru ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2012.

Ana gani dai ko da tabbas hukumomin Amurkan sun yi wa shugabannin Faransan leken asiri, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ba zata tabbatar da hakan ba.

Sai dai bayanan da shafin na Wikileaks ya kwarmata a baya a game da leken asirin da aka yi wa shugabannin Jamus da Brazil da Mexico, sun sa ana gani da alamun gaskiya a bayanan da shafin ya kwarmata yanzu.

Daya daga cikin bayanan da shafin na Wikileaks ya wallafa yanzu, ya nuna yadda shugaba Hollande na Faransa ya amince da wasu tarurruka na sirri, inda aka tattauna batun ficewar kasar Girka daga kungiyar kasashe masu amfani da kudin bai daya na Yuro a shekarar 2012.