Kasashen turai za su karbi bakin haure

Migrants Hakkin mallakar hoto
Image caption Migrants

Bayan kwashe sa'o'i da dama shugabanin kasashen turai suna tattaunawa sun amince da su karbi dubban bakin haure wadanda suka isa nahiyar turai.

Babu wata matsaya da aka cimma akan yawan bakin hauren da za a dauka a taron.

Bakin haure dubu arba'in ne wadanda suka tsallaka ta kogin baharrum za a kawashe su daga Girka da kuma Italia nan da watanni biyu masu zuwa.

Za kuma a tsugunnar da wasu karin bakin hauren dubu ashirin wadanda yakin basasa ya raba su da muhallansu.

Mai magana da yawun Firaministan Hungary ya shaidawa BBC cewa akwai bukatar ayi wani abu akan batun tudadowar bakin haure cikin kasar sa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba