Ndume da Na'Allah sun samu mukami

Hakkin mallakar hoto bukola
Image caption Sanata Saraki na fuskantar matsin lamba daga jam'iyyar APC

Shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki ya sanar da sunayen shugabanni uku daga cikin hudu na jam'iyyar APC mai mulki.

Saraki ya karanto wasika a zauren majalisar, inda ya bayyana Sanata Muhammed Ali Ndume daga arewa maso gabas a matsayin shugaban masu rinjaye, sai Sanata Bala Ibn Na'Allah daga arewa maso yamma a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.

Sanata Saraki kuma ya karanto sunan Sanata France Alimikhena daga Kudu maso kudancin kasar a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.

Wannan matakin ya saba da matsayin da uwar jam'iyyar APC ta fitar inda ta bukaci a bai wa Sanat Ahmed Lawan mukamin shugaban masu rinjaye da kuma Sanata George Akume a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.