Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Issoufou ya sha alwashin hada hannu domin yaki da Boko Haram

Dakarun jamhuriyar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram 15 a luguden wuta ta sama da kasa da suka kaddamar.

Dakarun sun kai samamen ne a kusa da kan iyakar kasar da Nigeria.

Sojojin sun ce kuma sun kama fursinoni kusan 20 tare da lalata babura da motocin mayakan.

Hakan ya biyo bayan harin da 'yan Boko Haram suka kaddamar a kauyen Yebbi da ke yankin Bosso a ranar Laraba da safe.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewar ya kirga gawarwaki biyar sakamakon harin na Yebbi.

Nijar na daga cikin kasashen da suka hada rundunar hadin gwiwa domin kawar da Boko Haram tare da Nigeria da Chadi da Kamaru da kuma Benin.