Obama ya gayyaci Buhari zuwa Amurka

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Buhari ya halarci taron G7 a Jamus

Fadar White House ta Amurka ta ba da sanarwar cewa Shugaba Obama ya gayyaci Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Sanarwar da Fadar White House ta fitar na cewa Shugban Amurka Barrack Obama zai karbi bakuncin Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a fadar White da ke Amurka ranar 20 ga watan Yuli.

Sanarwar ta ce ziyarar za ta kara jaddada dadaddiyar zumuntar da ke tsakanin Amurka da Nigeria, tare da kuma kudurin da Amurka ke da shi na karfafawa da kuma bunkasa wannnan zumunta tare da sabuwar gwamnatin Nigeria.

Sanarwar ta ce a lokacin ganawar, Shugaba Obama zai tattauna tare da Shugaba Muhammadu Buhari a kan abubuwan da kasashen biyu ke baiwa fifiko, ciki kuwa har da hulda da ke tsakanin Amurka da Nigeria domin bullo da wata manufa ta bai daya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Akwai kuma yunkurin Nigeria na aiwatar da sauye-sauyen ta fuskar tattalin arziki da siyasa wadanda za su taimakawa kasar kaiwa ga matsayinta na shugaba a yankin.