Buhari ya rushe hukumar zartarwar NNPC

Image caption Ana zargin tafka cuwa-cuwa sosai a NNPC

Shugaba Muhammadu Buhari ya rushe hukumar zartarwa ta babban kamfanin mai na kasar NNPC nan take.

Wata wasika dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Danladi Kifasi ta ambato shugaban ya na godiya ga mambobin hukumar saboda aikin da suka yi wa kasa.

Bisa tsari dai, ministan albarkatun man fetur ne ke shugabantar hukumar zartarwar NNPC wanda ke lura da harkokin man kasar.

A cikin 'yan shekarun nan dai NNPC ya kasance inda ake zargin ana wadaka, da kuma zarge-zargen badakalar cin hanci da rashawa.

Daga cikin 'yan hukumar da aka rushe akwai Mr. Steven Oronsaye, tsohon shugaban ma'aikata da kuma manajan darektan NNPC, Dr. Joseph T. Dawha.