Buhari ya yi sallar Juma'a a Aso Rock

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Buhari ya sha alwashin mai do da martabar Nigeria

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Sallar Juma'a a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja.

Shugaban ya yi hakan ne saboda sawwake wa mutane wahalhalun da suke shiga sakamakon rufe hanyoyi bisa dalilan tsaro duk lokacin da shugaban kasa zai je babban masallaci na Abuja.

Sanarwa daga Kakakin shugaban kasar, Femi Adeshina ta ce daga yanzu shugaba Buhari zai fi yin Sallar Juma'a ne a fadar Aso Rock tare da sauran musulmi.

Lokaci zuwa lokaci, shugaba Buhari zai dinga zuwa babban masallacin Abuja domin yin sallar Juma'a.

Wannan ne karon farko da ake Sallar Juma'a a fadar Aso rock.