An fille ma wani kai a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wurin da fashewar ya afku

'Yan sanda a Faransa sun ce an fille kan wani mutum kuma mutane da dama sun jikkata a wani hari da aka kaddamar.

Ana zaton kungiya mai fafutikar Islama ce ta kai harin a ma'ajiyar sinadirai da ke gabashin Faransa.

Kafofin yadda labarai na Faransa sun ce wata mota mai dauke da mutane da dama ta kutsa cikin wurin a wani bangaren masana'antu da ke kusa birnin Lyon kafin a ji karar fashewar.

'Yan sandan sun ce an kama wani mutun mai shekaru 30 a masana'antar, kuma sananne ne a wurin hukumar lekan asiri".

'Tuta'

Rahotanni sun ce an ga tutocin kungiyar masu fafitikar Islama a wurin.

An tsaurara tsaro a muhimman wurare a lardin kuma ministan cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve ya isa wurin da lamarin ya afku.

A 'yan mintunan da suka gabata shugaba Francois Holland na Faransa ya ce "Lamarin da ya afku da safe ya yi kama da hare-haren ta'addanci."

Ya kuma tabbatar cewa a samu wani mutum wanda aka fille kansa, wanda aka yi wani rubutu a kai.

Hollande ya ce ba ya kokwanton cewa sun kai harin ne da manufar rushe ginin.

Lamarin ya faru watanni biyar bayan da kungiyar masu da'awar kafa musulunci suka kai wani mummunan hari kan wani gidan mujalla da ke Faransa da kuma wasu hare-haren a ciki da kewayen birnin Paris.