Ambaliya ta hallaka mutane 70 a Indiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ambaliyar ruwa a Gujarat

Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya da ya haddasa ambaliyar ruwa, ya hallaka mutane a kalla 70 a jihar Gujarat da ke yammacin India.

Ma'aikatan ceto sun ce kusan mutane dubu 9 aka kwashe zuwa wuraren da ke kan tsaunuka a yankunan da lamarin yafi kamari.

Mafi yawan mace-macen da aka yi, ya faru ne lokacin da aka yi zaftarewar kasa kuma gidaje suka ruguje.

Jami'ai sun ce lamarin ya janyo lalacewar amfanin gona da kuma kadarori.