'Yan Afrika suna son yin jihadi - Rahoto

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ta'addanci na karuwa a yankin Afirka ta arewa

Wani rahoto da wata kungiya mai kula da tashe-tashen hankula a kashen duniya ta fitar ya yi gargadin cewa matakan da kasashen yammacin duniya suke dauka wajen dakile ta'addanci a yankin Afirka ta arewa, ba sa yin wani tasiri.

Kungiyar mai ofishi a Brussels ta ce ba zai zama aibu ba idan aka ayyana duk wani mai kaifin kishin addinin Islama da wanda idan ya samu dama zai iya yin jihadi.

Rahoton ya ce akwai matasa 'yan bana-bakwai masu dimbin yawa a kasar Nijar da Chadi da Libya wadanda sun gaza samun matakin ilimi mai zurfi, sannan kuma ba su da aikin yi.

Hakan ne in ji rahoton ya sanya mafi yawan matasan tunanin kwarara zuwa kasashen turai domin ci rani ko kuma kokarin yin jihadi.

Rahoton kungiyar ya kara da jan hankalin masu bada tallafi da su mayar da hankali kan raya kasashen yankin na Afirka ta arewa ta fannin samar da sahihin jagoranci kuma mai nagarta.