An hallaka mutane 37 a Tunisia

Image caption Dubban mutane ne ke zuwa yawon bude ido a Tunisia

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani otal da 'yan yawon bude ido ke zuwa kasar Tunisia, inda suka hallaka akalla mutane 27.

Hukumomin kasar sun ce jami'an tsaro sun hallaka daya daga cikin 'yan bindigar, yayinda kuma ake farautar dayan.

Harin ya faru ne a birnin Sousse, inda baki 'yan yawon bude ido da dama daga kasashen Turai da arewacin Afirka ke tururuwar zuwa.

Karo na biyu kenan ana kai harin a wurin 'yan yawon bude ido a kasar ta Tunisia.

A cikin watan Mayu ma, harin 'yan bindigar ya hallaka mutane fiye da 20 a gidan ajiye kayan tarihi na Bardo da ke Tunis, babban birnin kasar.