Burundi ta ce za a yi zaben kasar ranar Litinin

Burundi President Hakkin mallakar hoto
Image caption Burundi President

Wakilin Burundi a majalisar dinkin duniya ya ce za a gudanar da zaben kasar a ranar litinin kamar yadda aka tsara duk da kiran da sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban-ki Moon ya yi na a daga.

Mr Ban ya ce ya damu matuka da yanayin tsaro a Burundi inda shugaba Pierre Nkurunziza zai sake tsayawa a karo na uku, lamarin da ya janyo zanga-zanga akan tituna wacce aka shafe tsawon makonni anayi.

Jakadan Burundin Albert Shingiro ya shaidawa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya cewa akasarin 'yan kasar na son a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Tuni dai jam'iyyun adawar kasar suka sanar da kauracewa zaben.