An ceto kwarorin da aka sace a Najeriya

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Mayakan sa-kai na yankin Niger Delta

Rundunar tsaro ta 'yan sandan a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ce ta samu nasarar ceto kwarorin nan biyu 'yan kasar Lebanon da aka sace kwanaki uku da suka gabata, a yankin Niger Delta.

Rundunar ta samu nasarar ceto mutanen ne bayan yiwa masu garkuwar kofar rago a karamar hukumar Ogbia, a jihar ta Bayelsa.

Jihar Bayelsa dai na daya daga cikin jihohin da ke yankin Niger Delta mai albarkatun man fetur.

A baya dai yankin na Naija Delta ya yi kaurin suna wajen yin garkuwa da mutane inda a wasu lokuta har sai an biya diyya kafin su saki mutane, akasari 'yan kasashen waje.