Za a rufe Masallatai a Tunisiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dai kashe wanda ya kai harin

Hukumomi a kasar Tunisia sun ce za su rufe masallatai har guda 80 a fadin kasar bisa zargin koyar da mugunyar akida wadda ke sanya mutane zama masu tsattsauran ra'ayi.

An ce akalar masallatan dai ba ta hannun gwamnatin kasar.

Dangane kuma da mutanen da harin ya rutsa da su, firaiministan kasar Tunisia, Habib Essid ya ce mafi yawancin su 'yan asalin kasar Birtaniya ne da Jamus da kuma Belgium.

Tuni dai kungiyar IS dauki alhakin kai wannan hari, a shafinta na kafar sada zumunta. Kungiyar ta bayyana wanda ya kai harin da Abu Yahya Alqairawaniy.

Sai dai kuma hotunan bidiyo na kamerar tsaro ta CCTV sun nuna cewa wani dalibi ne mai suna Saif al-Din al'Rizgi shi ya kai harin.

Jami'an tsaro da wadanda suka shaida al'amarin sun fada wa BBC cewa maharin mutum daya ne wanda kuma bai wuce shekaru 20 da doriya ba. Kuma an kashe shi bayan harbinsa da jami'an tsaro suka yi a lokacin da yake kokarin tserewa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba