'Yan yawon bude ido na gudu daga Tunisia

Hakkin mallakar hoto

Ana kwashe dubban 'yan yawon bude ido daga Tunisia, domin fitar da su daga kasar bayan harin da aka kai a wani wurin shakatawa na gabar kogi.

Harin, wanda aka kai ranar Asabar, ya hallaka akalla mutane 38, galibinsu Turawa 'yan kasashen yamma.

A filin jirgin saman Hammamet da ke kusa da Tunis masu yawon bude ido da suka je hutu sun yi layin shiga jirgi domin barin kasar.

Gwamnatin Tunisia ta ce an tsaurara tsaro a wuraren yawon bude ido.

Hakan nan kuma gwamnatin ta ce za ta rufe masallatai 80 wadanda ake zargi da yin wa'azin da ke tada hankali.

Hukumomin Tunisian sun ce akasarin wadanda aka kashe a harin 'yan Burtaniya ne.

Sun ce za su dauki matakai domin tinkarar matsalar.

Fira-ministan Burtaniya David Cameron ya ce dole 'yan kasarsa su shirya ma fuskatar cewa sun yi asarar rayuka da yawa.

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai harin. An dai harbe dan bindigar da ya kai harin.

Karin bayani