An kama mutane 100 saboda yin fitsari a India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kuma aika wadanda aka kama zuwa gidan kaso

'Yan sanda a arewacin India sun kama mutane sama da 100 bisa laifin yin fitsari a kusa da tashar jirgin kasa.

Hakan ya faru ne sakamakon kin amincewa da zarnin fitsarin da ke addabar ma'aikatan hukumar jirgin kasa a birnin Agra.

Hakan ne yasa hukumar ta kaddamar da yaki da wannan al'ada ta fitsari a wurare da kuma cikin jama'a.

'Yan sanda sun kai samame wuraren da ake fitsarin sun kuma yi babban kamu a inda suka cafke masu fitsarin fiye da dari, aka kuma yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na tsawon kwana guda.

A kasar India dai biyan bukata musamman yin fitsari a jikin garu da bishiyoyi kuma a cikin jama'a ba wani abun kyama ba ne a tsakanin maza musamman ma matasa.