Al Shabaab ta kashe mutane 10 a Somalia

Image caption Al Shabaab ta matsa kaimi wajen kai hare-hare.

Rahotanni daga kudancin Somalia sun ce kungiyar Al Shabaab ta masu da'awar jihadi sun kai farmaki kan wani sansanin soji, inda suka hallaka sojoji 10.

Shaidu sun ce an gwabza kazamin fada a kusa da sansanin dake birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa.

Kungiyar ta Al Shabaab ta matsa kaimin kai hare-hare a kasar Somalia da kuma dakarun kungiyar tarayyar Afirka AU, a lokacin wannan wata da musulmai ke azumin Ramadan.

Mazauna kudancin yankin Shabelle sun ce dakarun kungiyar ta AU sun janye daga sansanoninsu da dama a can.

Har yanzu dai babu wasu bayanai da suka fito daga dakarun na kungiyar ta AU.