Taron karrama mawakan zamani

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sam Smith ya zama tauraron gasar fitattun mawaka bakar fata, watau BET Awards.

Sam Smith ya zama tauraro a gasar fitattun mawaka bakar fata, watau BET Awards, ita kuma Nicki Minaj ta samu kyauta a gasar salon wakar rap.

Sam Smith ya yi nasara a gasar BET ta wannan shekarar, wacce aka yi a birnin Los Angeles na Amurka.

Bai halarci bikin da aka shirya a Los Angeles ba, saboda haka Anthony Anderson, wani tauraron wasan kwaikwayo, ya karbi kyautar a madadin sa.

Anthony ya ce "Sam Smith bai zo taron nan ba saboda shi farar fata ne, kuma bai yi tunanin zai yi nasara a wannan gasa ta BET Awards ba. Amma mun nuna masa mu ma muna kaunar sa".

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan shine karo na shida a jere da Nicki Minaj take cin gasar tauraruwar mawakiya salon hip-hop.

Wannan shi ne karo na shida a jere da Nicki Minaj take cin gasar tauraruwar mawakiya salon hip-hop, kuma ta taho da mahaifiyar ta domin karbar kyautar.

Ta yi wa matashin da ke waka salon rap, Def Loaf, godiya wanda shi ma ya yi takara a gasar, da kuma saurayinta -- shi ma mawakin salon rap, Meek Mill, wanda ke zaune a gefen ta cikin taron, ta kuma yi wa mahaifiyarta godiya.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kendrick Lamar shi ya fara shirye-shiryen BET Awards din da wakar sautin rap,

Kendrick Lamar, shi ya fara shirye-shiryen BET Awards din da waka mai sautin rap, inda aka biyo shi da tutar Amurka a baya.

Daga baya ya yi nasarar samun lambar kyautar fitaccen mawakin salon hip-hop a bangare maza.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Terrence Howard fitaccen dan wasan kwaikwayo ne kuma ya samu kyautar fitaccen dan wasa namiji.

Terrence Howard, shi ma fitaccen dan wasan kwaikwayo ne, kuma ya samu kyautar fitaccen dan wasa na miji domin rawar da ya taka a wani wasan kwaikwayo mai suna Empire, wanda ake nuno wa a tashar Fox.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption P.Diddy ya fada wani rami yayinda yake rera wakar sa a wurin ba da kyautar.

Mawakin salon rap, wanda aka fi sani da P.Diddy ya fada wani rami, yayin da yake rera wakar sa a wurin ba da kyautar.

Lil Kim da Mase da Faith Evans da 112 da kuma The Lox, su ma mawakan salon rap ne; sun hau dandalin wakar, suka bi P.Diddy domin taya shi rera wakokin, wadanda suka hada da Peaches and Cream da Bad Boy.

An fito da faifen bidiyon mawakin nan da ya rasu, watau Notorious BIG, inda aka nuno shi yana rera wakar Mo Money Mo Problems.

Wannan dandalin waka da P.Diddy ya shigo shi ne fitowarsa ta farko a fili, tunda jami'an tsaro suka kama shi ranar Litinin din da ta gabata bisa laifin amfani muguwar makami.

Mawaki Chris Brown ya hau kan dandalin; shi ma ya rera wakoki kala-kala, ya kuma samu lambobin yabo guda biyu -- ta fitaccen mawakin salon R&B/pop artist, da kuma wadda ake cewa Fandemonium Award.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An yi wa fitacciyar mawakiyar nan, Janet Jackson daukaka ta musamman a wannan taro.

Janet Jackson, ita ma fitacciyar mawakiya, ta samu daukaka ta musamman, inda ta dade ba ta fito bainar jama'a ba amma ta fito ta karbi lambar yabo.

Janet Jackson tana shirin fitowa da sabon faifan wakoki, kuma za ta zagaya wasu kasashen waje domin ta rera wakokin nata.

Sauran mawakan da suka samu lambar yabo, sun hada da Beyonce, wacce aka bai wa fitacciyar mawakiyar salon R&B/Pop mace, kuma an hada mata da kasaitaccen faifan bidiyo.

Rae Sremmurd kuma an ba su lambar yabo ta fitacciyar kungiya mawaka da Common da John Legend, wadanda hadin gwiwarsu ta sa suka samu lambar yabon fitattu kan wakar hadin gwiwa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An taka rawar gani a taron BET Awards a birnin Los Angeles a Amurka.

Shi kuwa Mo'Ne Davis an ba shi lambar yabon fitaccen mawaki cikin matasa.