An bude runfunan zaben a Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza

An bude runfunan zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Burundi duk da makonnin da aka kwashe ana tashin hankalin a kasar saboda yunkurin shugaba Pierre Nkurunziza na neman ta zarce karo na uku.

'Yan adawa a kasar sun kaurace wa zaben, sannan Tarayyar Afrika ta ce ba zata tura jami'anta masu sa ido ba saboda rashin ka'idoji na gudanar da zabe na gaskiya.

Rahotannin sun ce akwai yanayi na fargaba a babban birnin kasar Bujumbura.

A jiya Lahadi, shugaban majalisar dokokin kasar Pie Ntavyohanyuma ya ce ya fice daga kasar saboda tsoron kada a halakashi bayan ya bukaci shugaban kasar da ya hakura da sake tsayawa takara.