Bama bamai sun tashi a Chadi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tashin bama baman ya faru ne makonni kadan bayan aukuwar wani, wanda ya kashe a kalla mutane 38.

Rahotanni daga Chadi na cewa bama bamai guda biyu sun tashi a N'Djamena, babban birnin kasar, inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 11.

Mazauna birnin sun ce bam din farko ya tashi ne da sassafe a unguwar Dinguessou, yayin da bam na biyu ya tashi mintuna shida bayan na farko.

Mazauna birnin da dama sun shaida wa BBC cewa cikin mutanen da suka mutu har da 'yan sanda biyar.

Har yanzu dai hukumomi ba su ce komai dangane da harin bama baman ba.

Wannan lamari dai na faruwa ne makonni kadan bayan wani harin bam da ake zargin 'yan Boko Haram da kai wa ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 38, sannan ya raunata mutane 100.