'Yan matan Chibok sun shiga Boko Haram'

Image caption Har yanzu ba a ceto 'yan matan na Chibok ba.

Wasu sun shaida wa BBC cewa an tilasta wa 'yan matan Chibok da aka sace daga jihar Borno ta Najeriya shiga kungiyar Boko Haram.

Shaidun sun nuna cewa yanzu 'yan matan na cin zarafin mutanen da ake kamawa, ko ma su kashe su da kansu.

Har yanzu dai ba a gano matan 219 ba, fiye da shekara guda tun bayan da aka sace su daga makarantarsu da ke Chibok, a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya.

Mata uku da suka yi ikirarin cewa an tsare su a sansanin da aka tsare 'yan matan Chibok sun shaida wa shirin BBC Panorama cewa an cusa wa 'yan matan na Chibok tsattsauran ra'ayi, kuma yanzu suna hukunta mutanen da aka kama.

Miriam (ba sunanta a ainihi ba ne), mai shekaru 17, ta tsere daga sansanin na Boko Haram, bayan an tsare ta har watanni shida.

Ta ce an tilasta mata auren wani dan kungiyar Boko Haram, kuma yanzu haka tana da ciki.

Da take bayyana kwanakinta na farko a sansanin, Miriam ta ce: "Sun gaya mana cewa mu shirya, domin kuwa za su aurar da mu".

Ta kara da cewa ta hadu da 'yan matan Chibok, ko da yake an ajiye su a wani gida na musamman.

Miriam ta ce ta ga 'yan matan na Chibok kwanaki kadan kafin ta tsere daga hannun 'yan Boko Haram.

Ta kara da cewa ta gan su ne rike da bindigogi.

Gwamnatin Najeriya dai ta kaddamar da wani shiri na sauya tunanin mutanen da suka kubuta daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.