Masar: Mai Shigar da Kara ya Mutu

Hakkin mallakar hoto AP

Mai gabatar da kara na Masar, Hisham Barakat, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a harin bam na mota da aka kaiwa kwambar motocinsu a birnin Alkahira.

An kai musu harin ne lokacin da suke bi ta wata hanya a gundumar Heliopolis.

Girman fashewar ya lalata motoci da shaguna da dama, kana masu tsaron lafiyar Hisham Barakat biyu sun samu raunuka.

Marigayin dai ya sha kai masu kaifin kishin Islama gaban kuliya, tun bayan da sojoji suka tumbuke gwamnatin shugaba Mohammed Morsi a shekara ta 2013.

Wata kungiya da ba a san da ita sosai ba da ake kira ''Popular Resistance of Giza'' ta ce ita ta kai harin.