Za a gwada na'urar takaita saurin mota

Image caption Motar safa a Birtaniya

Za a yi gwajin wata sabuwar na'ura ta takaita saurin motocin safa a kan wasu hanyoyin mota a London da nufin kara kiyaye haduran ababen hawa.

Na'urar mai suna Intelligent Speed Application (ISA) za ta rika amfani da hanyar sanin wurin da abubuwa suke ta GPS da aka makala a cikin motocin.

Na'urar za ta rika bayar da bayanai game da inda motocin suke, da kuma irin saurin da suke yi idan suna tafiya, tare kuma da takaita saurin injinan motocin.

Fiye da mutane 1800 ne kodai suka mutu ko kuma suka samu munanan raunuka sakamakon hadarin motocin safa na bus a London cikin shekaru 5.

Daga cikin watan Yuli ne za a fara amfani da nau'rar a cikin motoci 47.

Na'urar za ta bai wa direbobi damar mayar da hankulan su ga sauran abubuwa masu kawo hadari, a maimakon koda yaushe su rika duba irin saurin da suke yi.