Nigeria: Mutane sun yi tururuwa a bankuna

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Babban bankin Najeriya

A Najeriya, daruruwan mutane sunyi turuwa zuwa bankuna domin suyi rigista rana daya kafin wa'adin da babban bankin kasar ta sanya ya kawo karshe.

Babban Bankin dai ya yi gargadin cewa duk wanda ba a tantance shi ba, ba zai iya cire kudi daga asusunsa.

An dai fara tantacewar masu asusun ajiya a banki ne a shekara daya da rabi da ta wuce.