Boko Haram: Chadi ta kama mutane 60

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Chadi Idriss Deby

Jami'an tsaro a kasar Chadi sun ce an kama mutane 60 da ake zargi da hannun a harin da aka kai N'djamena wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 38 tare da raunata wasu da dama.

Mai gabatar da kara na kasar Chadi, Alghassim Khamis ya ce mutanen da aka kama sun hada da wasu 'yan kasashen kamaru da Najeriya da kuma Mali, haka kuma akwai wasu 'yan Chadin cikin wadanda aka kama.

Inda ya kara da cewa "An gano maboyar 'yan ta'adda an kuma lalata shi, yayin da aka gano wasu na'urorin sadarwa. "

Haka kuma ya Khamis ya ce burbushin da aka tattara a wuraren da aka kai harin ya nuna cewa an yi kyakkyawan shiri kafin kai harin.

A ranar 15 ga watan Yuni ne dai wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam din da ke jinkinsa a wajen wani offishin 'yan sanda, yayin da wasu 'yan kunar bakin waken biyu kuma suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a kusa da wata makarantar 'yan sanda.

Harin shine na farko da aka kai N'Djamena, babban birnin Chadi.

Chadi ta kasance wata babbar kawar Najeriya a wajen yaki da kungiya Boko Haram, haka kuma shugaban kungiyar Boko Haram ya taba yin barazana ga shugaban Chadi tare da shan alwashin yin ramuwar gayya.

Bayan kwanaki da kai harin ne kuma Chadi ta ce ta kai farmaki kan sansanonin Boko Haram.