Taurarin da suka fi samun kudi a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan dambe, Floyd Mayweather da Manny Pacquiao, su ne gaba a jerin sunayen taurari na mujallar Forbes.

'Yan dambe Floyd Mayweather da Manny Pacquiao sune na gaba a jerin sunayen taurari na mujallar Forbes wadanda aka fi biyan albashi mai tsoka a duniya

Sunayen 'yan dambe Floyd Mayweather da Manny Pacquiao na cikin jerin sunayen taurari 100 na duniya wadanda suka fi samun albashi mai yawa.

An kyiyasta fadan da suka yi yasa Mayweather ya samu dala miliyan 300 a cikin watannin 12 da suka wuce.

Pacquiao ne ya kasance na biyu inda ya samu dala miliyan 160, amma kuma ba'a bayyana jimillar kudaden karshe da suka samu a fadan ba.

An gina kiyasi na mujallar Forbes ne a kan abinda masana suka bayyana a matsayin damben da aka fi kashewa kudi a tarihin dambe.

Natalie Robehmed ma'aikaciyar Mujallar Forbes ta ce "Dala miliyan 300 da Mayweather ya samu ya sauya tarihin da aka kafa akan wanda ya fi samun kudi a masu wasa, wanda a baya Tiger Woods ya rike kuma ya ajiye dala miliyan 115 a shekarar 2008." "It is above and beyond anything anyone has ever done."

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayweather ya hada kambun WBO akan na WBC da WBA da ya riga ya lashe.

Floyd Mayweather ya yi galaba a kan Manny Pacquiao a ranar 3 ga watan Mayu a garin Las Vegas. Kewayar yin waka wanda Katy Perry ta yi ya taimaka mata wajen daukan matsayi na uku inda ta samu dala miliyan 135, sai kuma kungiyar One direction wadda suka biyo baya da dala miliyan 130 Sai gidan talabision na Amurka da kuma ma'aikacin gidan rediyo da talabijin Howard Stern wanda ya samu dala miliyan 95.

Mawaka da masu wasan guje-guje da tsalle-tsalle sun mamaye gurbi 10 da ke kan gaba wadanda suka hada da mata 2. Tauraro kuma mawaki, Garth Brooks shine a matsayin lamba 6 inda ya samu dala miliyan 90, yayin da Taylor Swift ya dauki matsayi na 8 inda Tauraron Fim din Iron Man, Robert Downey karami ya samu dala miliyan 80.

Marubuci James Patterson yana matsayi na bakwai inda ya samu dala miliyan 89 kuma dan kwallo Cristiano Ronaldo yana matsayi na 10 a kan dala miliyan 79.5.

Mujallar Forbes ta harhada sunaye na shakera na taurarin da suka yi fice na wassani da talabijin da wake-wake da kuma marubuta inda ta yi kiyasin kudaden da suke samu kafin a cire haraji na tan Wuni na shekarar 2014 zuwa Wunin shekarar 2015.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto EPA
Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Taurariya Kim Kardashian.

Ba'a cire kudaden gudunarwa da na wakilai da kuma na shari'a ba. Tauraruwar wani shirin Talabijin na Amurka, Kim Kardashian, wace ta samu dala miliyan 28 a jerin sunaye na baya, ta samu kusan ribanya kudaden ta zuwa kiyasin dala miliyan 52.5 da Forbes ta yi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto AP

Jennifer Lawrence da Scarlett Johansson wadanda suka samu matsayi na 65 da dala miliyan 35.5 sune kawai mata biyu na 'yan wasan fim da sunayen su ya fito a jerin sunaye 100 idan aka kwatanta da 'yan wasan fim maza.

Hakkin mallakar hoto Getty

Tauraron masu girke-girken abinci Gordon Ramsay na lamba na 21 da ya samu dala miliyan 60 shine ne kadai mai girka abin da sunan shi ya fito a cikin jerin sunayen, wadanda suka hada da mawaka 38 da masu wasa 29, a mutane 6 da masu barkwanci 2.

Calvin Harris ne a matsayi na 17 akan dala miliyan 66 da Ed Sheeran ya samu matsayi na 27 da albashin dala miliyan 57.

Lewis Hamilton ne a matsayi na 55 da dala miliyan 39 sai kuma Gareth Bale's a matsayi na 67 da albashin dala miliyan 35.