Girka ta nemi karin wa'adin biyan bashi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Girka tana bukatar a sauya fasalin yadda take biyan bashi.

Kasar Girka ta bukaci Tarayyar Turai ta kara mata wa'adin shekaru biyu domin ta samu damar iya biyan bashin da ake bin ta.

Haka kuma kasar tana bukatar a sauya fasalin biyan bashin ta yadda ba za ta rika biya a jere ba.

Da fari dai, kasar ta Girka ta tabbatar da cewa ba za ta iya cika wa'adin da aka dibar mata na zuwa karshen ranar Talata.

Ministocin kungiyar Tarayyar Turai za su tattauna a game da bukatar Girka, a taron da za su yi ta wayar tarho idan anjima.

Sai dai tun kafin lokacin, Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce ba za a samu sauyi ba dangane da matsayinsu a kan bashin da ake bin Girka.