Wa'adin aikin Jega ya kare a INEC

Image caption 'Yan Najeriya da ma kasashen duniya sun yaba wa Jega saboda zaben da ya gudanar.

Farfesa Attahiru Jega da kwamishinonin hukumar zaben Najeriya guda shida sun yi ritaya bayan wa'adin aikinsu a hukumar ya kare ranar Talata.

Farfesa Jega ya kwashe shekaru biyar yana shugabantar hukumar zaben ta Najeriya.

A wani takaitaccen biki da aka gudanar a hedikwatar hukumar zaben da ke Abuja, Farfesa Jega ya mika ragamar hukumar ga kwamishinan zabe, Mohammed Wali daga jihar Sokoto, wanda zai yi shugabancin riko na hukumar.

Tshohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya nada Farfesa Jega a watan Yunin shekarar 2010, domin maye gurbin Farfesa Maurice Iwu.

Farfesa Jega ya gudanar da manyan zabukan kasar guda biyu - na shekarar 2011 da na 2015.

Bayan zaben da ya gudanar a watannin Maris da Afirilun shekarar 2015 ne, Jega ya ce ba zai nemi a tsawaita wa'adinsa na shugabancin hukumar zaben ba.

Ana kallon zabukan a matsayin daya daga cikin wadanda suka fi inganci da aka gudanar a kasar.