Bankunan Nigeria sun yi cikar-kwari

Image caption Babban Bankin Najeriya ya ce mutane za su fuskanci kalublae waje cire kudi idan ba a tantance su ba.

Masu hulda da bankuna sun yi tururuwa zuwa rassan bankuna daban-daban a Najeriya a yayin da wa'adin da Babban Bankin kasar na rajistar masu asusu ke cika a ranar Talata.

An kafa dogayen layuka a bankunan a kokarin da mutane ke yi na ganin sun yi rajistar kafin karewar wa'adin.

Babban Bankin ya ce ya dauki matakin yin rajistar masu hulda da shi ne domin rage yawaitar zamba-cikin-aminci da kare satar kudin mutane.

A cewar babban bankin, duk wanda ba a tantance a karshen ranar Talata ba zai fuskanci matsala wajen samun damar yin amfani da asusunsa ba.