Za a binciki kudin da NNPC ya karkatar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin jami'an kamfanin NNPC da wawashe kudaden mai

Majalisar koli kan tattalin arziki da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya kaddamar, za ta gudanar da bincike kan yadda kamfanin mai na kasar, NNPC ya karkatar da wasu kudade da yawan su zai kai Naira Tiriliyan Uku da rabi.

Ana zargin cewar kamfanin ya karkatar da wadannan kudade ne a cikin shekaru uku da suka gabata.

A ranar Litinin ne aka kaddamar da majalisar da nufin bayar da shawarwari game da yadda za a farfado da tattalin arzikin kasar.

Kwamitin na karkashin jagorancin mataimakin Shugaban Farfesa Yemi Osibanjo

Majalisar tattalin arzikin ta kara kwamitin mambobi hudu wanda zai binciki yadda kamfanin NNPC ya yi amfani da wadannan kudade.